logo

HAUSA

Abbas Ibrahim: Sin kasa ce mai ban al’ajabi

2023-03-21 15:58:32 CMG Hausa

Malam Abbas Ibrahim, dalibi ne dake karatun digiri na uku a halin yanzu a kasar Indiya, kuma ma’aikaci ne a jami’ar jihar Bauchi dake tarayyar Najeriya.

Duk da cewa malam Abbas Ibrahim bai taba zuwa kasar Sin ba, amma ya dade yana sauraren shirye-shiryen sashin Hausa na gidan rediyon kasar wato CRI, kuma ya san abubuwa da yawa game da kasar. 

A zantawar sa da Murtala Zhang, malam Abbas Ibrahim ya yi tsokaci kan ci gaban da kasar Sin ta samu, inda ya bayyana wasu fannonin hadin-gwiwa da ya ce ya dace a yi tsakanin Najeriya da kasar Sin.

A karshe, malam Abbas ya bayyana fatan sa a nan gaba, idan ya kammala karatu a kasar Indiya. (Murtala Zhang)