logo

HAUSA

Yadda ake tace ruwan teku a birnin Qingdao

2023-03-21 19:28:32 CMG Hausa

Ga yadda ake tace ruwan teku a birnin Qingdao na lardin Shandong da ke gabashin kasar Sin, don ya zama ruwa marar gishiri, wanda al’umma ke iya amfani da shi a zaman rayuwarsu. Kasancewar birnin na Qingdao mashigin teku, cikin ‘yan shekarun baya, ya yi ta kokarin bunkasa ayyukan tace ruwan teku, don kara samar da ruwan da mazauna birnin ke amfani da shi. Yanzu haka kusan kaso 1/10 na ruwan da mazauna manyan sassan birnin ke amfani da shi ana samar da shi ne ta hanyar tace ruwan teku. (Lubabatu)