Vladimir Putin: Alakar Rasha da Sin abin koyi ne a hadin gwiwa cikin jituwa da kirkire-kirkire tsakanin manyan kasashe
2023-03-20 19:36:49 CMG Hausa
A gabannin ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a kasar Rasha, takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, ya wallafa wani bayani mai taken "Rasha da Sin—dangantakar abokantaka mai kyakkyawar makoma" a cikin jaridar People's Daily ta kasar Sin a ranar 20 ga watan nan, inda a cikin sa ya gaishe da jama’ar kasar Sin cikin aminci. Ya kuma bayyana cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen Rasha da Sin, wani abin koyi ne na hadin gwiwa cikin jituwa, da kirkire-kirkire a tsakanin manyan kasashe, yana kuma fatan shawarwarin da da zai yi da shugaba Xi Jinping, za su kara sanya sabon kuzari cikin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu daga dukkan fannoni.
Putin ya bayyana a cikin bayanin cewa, ziyarar ta shugaba Xi Jinping tana da babbar ma'ana, wadda ta sake tabbatar da cewa, dangantakar dake tsakanin Rasha da Sin ta kasance ta musamman, kuma a ko da yaushe, ta dogara ne kan amincewa da juna, da mutunta mulkin kai da moriyar juna.
Bayanin ya ce, ko da yaushe kasashen Rasha da Sin, suna dukufa wajen kafa tsarin tsaro na shiyya-shiyya, da na duniya baki daya, wanda zai zama daidai, a bude, kuma ba za a goyi bayan hari kan bangare na uku ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)