logo

HAUSA

Hukumar INEC za ta kammala sanar da sakamakon zaben gwamnoni a Litinin

2023-03-20 13:55:52 CMG Hausa

Yau Litinin 20 ga wata, ofisoshin hukumar zabe dake jihohi 28 da aka gudanar da zaben gwamnoni da na ’yan majalissun jahohi za su karkare sanar da sakamakon zabukan.

Tun a daren jiya Lahadi akasarin ofisoshin suka kammala sanar da sakamakon zaben wanda aka fara kirgawa tun da daren Asabar 18 ga wata.

Daga tarayyar Najeriya Wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Kamar yadda sakamakon ya kasance tun da karfe biyu na daren jiya Lahadi, agogon Najeriya, jahohin Yobe da Ogun da Gombe da Jigawa da Kwara da kuma Legas, turawan zaben jahohin sun tabbatar da nasarar ’yan takarar jam’iyyar APC.

Sauran jahohin da jam’iyyar APC mai mulkin kasar ta sami nasara a zabukan gwamnonin sun hada da Sokoto da Katsina da Borno  da kuma Ogun.

Haka kuma jam’iyyar PDP ta samu nasara a jahohin Rivers da Oyo da Akwa Ibom kamar yadda sakamakon daren jiya Lahadi ya nuna.

Haka kuma tun a  jiyan turawan zaben jahohin Plato da Enugu da Ebonyi suka sanar da dage ci gaba da bayyana sakamakon zuwa yau din nan Litinin 20 ga wata yayin da kuma a jihar Adamawa, matsalolin satar akwatina a wasu cibiyoyin zabe dake FUFORE sun haifar da tsaiko wajen kammala sanar da sakamakon zaben wanda ake fafatawa tsakanin ’yar takara daya mace a Najeriya Aishatu Binani da kuma dan takarar jam’iyyar PDP.

Koma dai me ake cikin tun daga safiyar wannan rana ta Litinin ’yan Najeriya za su kammala sanin mutanen da suka yi nasara a zaben na gwamna na ranar 18 ga wata, zaben da wasu daga cikin masu sa ido ke bayyana shi da cewa yana cike da matsaloli na tashe-tashen hankula da kuma rashin adalci.

Ko a daren na Lahadi 19 ga wata, hukumar zabe ta Najeriya mai zaman kanta ta tabbatar da cewa ya zama  wajibi  dai ta dauki matakai tsaurara wajen bibiyar korafen-korafen cin zarafin ma’aiaktanta da aka yi tare da tayar da hargitsi yayin zabukan a jahohin daban-daban na kasar.

Daraktan wayar da kan masu zabe na hukumar Mr Festus Okoye shi ne ya tabbatar da hakan yayin wani taron manema labarai, ya ce ma’aikatan hukumar da kuma ma’aikatan wucin gadi da hukumar ta dauka sun fuskanci cin zarafi a rumfunan zabe daban daban.

Kamar dai yadda ya ce, wasu daga cikin ma’aikatan ma yanzu haka suna kwance a asibiti, wasu sun kuma rasa rayukansu yayin da wasun kuma aka keta haddin su a bainar jama’a, inda ya ce ko kadan hukumar ba za ta barin wannan ya tafi haka kawai ba ba tare da an bibiyi hakkin ma’aikatan ba. (Garba Abdullahi Bagwai)