logo

HAUSA

An gudanar da taro kan yaki da talauci da samun bunkasuwar duniya na 2023 a lardin Yunnan na Sin

2023-03-20 14:03:26 CMG Hausa

An gudanar da taron dandalin tattaunawa kan yaki da talauci, da samun bunkasuwar duk duniya na shekarar 2023 a Nujiang, yankin kabilar Lisu mai cin gashin kansa dake lardin Yunnan na kasar Sin, inda jakadu da jami’an gwamanti, da masana fiye da 190 daga kasashe 20, da kungiyoyin kasa da kasa 4, ciki har da MDD suka yi musayar ra’ayoyi kan yaki da talauci, da fasahohin raya kauyuka, da zamanintar da kasa da kasa, da kuma samun bunkasuwa mai dorewa.

Hukumar kula da wallafa littattafai ta harsunan waje ta kasar Sin, da gwamnatin lardin Yunnan, da kungiyar huldar jama’a ta kasar Sin, da jami’ar Renmin ta kasar Sin, sun yi hadin gwiwa wajen karbar bakuncin gudanar da taron dandalin tattaunawar.

A gun taron, mahalartar taron sun yi tattaunawa kan taken “Yin hadin gwiwa wajen tsara taswirar farfado da kauyuka, da more sabuwar damar samun bunkasuwa tare da kasa da kasa”.

Shugaban hukumar kula da wallafa littattafai ta harsunan waje ta kasar Sin Du Zhanyuan ya bayyana cewa, yayin da ake yin kokarin sa kaimi ga fadada zamanintar da kasar Sin, Sin za ta yi hadin gwiwa tare da kasa da kasa wajen cimma daidaito, da kara yin hadin gwiwa, da maida hankali ga ayyukan yaki da talauci na kasa da kasa, don kara amfanar da jama’a. (Zainab)