An wallafa bayanin da Xi Jinping ya rubuta a kafofin yada labarai na kasar Rasha
2023-03-20 14:48:57 CMG HAUSA
A yau Litinin 20 ga wata, a gabannin fara ziyararsa ta aiki a tarayyar Rasha, aka wallafa bayanin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta, mai taken “Tinkarar kalubaloli tare: bude wani sabon babi na kara hadin kan Sin da Rasha, da samun bunkasuwa tare” a “Jaridar Rasha”, da shafin yanar gizo na kamfanin dillancin labarun kasar.
Bayanin ya nuna cewa, bunkasuwar dangantakar kasashen biyu, na bisa karfi daga zuciyoyin su a cikin daddaden lokuta. A cikin shekaru 10 da suka gabata, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban ta samu bunkasuwa sosai.
A bara, rikicin dake tsakanin Rasha da Ukraine ya tsananta. Sin na nacewa matsayin nuna adalci, da ingiza yin shawarwari tsakanin bangarorin masu ruwa da tsaki. Sin ta gabatar da takardar matsayin Sin game da warware rikicin Ukraine ba da dadewa ba, inda ta shigo da abubuwa masu dacewa da mahangar bangarori daban-daban. Sin ta yi imanin cewa, ba shakka za a iya warware rikicin, da tabbatar da kwanciyar hankali da tsaron duniya bisa hanyar da ta dace, idan bangarori masu ruwa da tsaki su hada kansu, da nacewa ga nuna adalci da daidaito, da daukar matakai masu dacewa.
Shugaba Xi ya kara da cewa, idan ana son taka rawa wajen warware batutuwan dake wakana a duniya, dole ne da farko, a daidaita matsalolin dake kasancewa a cikin gida yadda ya kamata. Ya ce “Muna cike da imanin cewa, Sin za ta ci gaba da ingiza sha’anin zamanintarwa irin na kasar Sin, da yin iyakacin kokarin samun bunkasuwa mai inganci, da ma kara bude kofa ga waje a nan gaba. Ba shakka, irin wadannan matakai za su baiwa dukkanin fadin duniya, ciki har da kasar Rasha sabbin damamaki na neman samun bunkasuwa. (Amina Xu)