logo

HAUSA

Sin ta fitar da rahoto game da halin dimokuradiyya a Amurka a shekarar 2022

2023-03-20 15:13:33 CMG HAUSA

 

A yau Litinin 20 ga wata, aka wallafa wani rahoto game da halin da demokuradiyyar Amurka ke ciki a shekarar 2022, a shafin yanar gizo na ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, inda rahoton ya gabatar da ainihin gaskiya mai dimbin yawa, tare da ruwaito ra’ayoyin da masana na kafofin yada labarai da dama suka bayyana, don tona hakikanin halin da kasar Amurka ke ciki a fannin demokuradiyya, wanda hakan ya fayyace matsalolin da Amurka ke fuskanta a wannan fanni, da rudani, da rikici, da ma kabalulolin da Amurka ta haifar wa duniya, saboda ta tilastawa sauran kasashe bin demokuradiyya irin tata.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fitar da wannan rahoto ne, domin al’ummomin duniya su iya samun damar sanin hakikanin ma’anar dimokuradiyya irin ta kasar Amurka.

Rahoton ya nuna cewa, a shekarar 2022, a kullum Amurka na fuskantar matsalolin rashin demokuraddiya, inda hukumomin siyasa ba sa iya taka rawarsu kamar yadda ake fata, har ta kai ba a iya samun jituwa tsakanin al’ummu daban daban a kasar. Matsalolin “gudanar da harkokin siyasa bisa amfani da kudi” da “amincewa da wani mutum bisa matsayin sa a siyasance” da tsananin gibin dake akwai tsakanin matalauta da masu arziki, da dai sauran matsaloli, sun kara tsananta.

Matsalolin da demokuradiyya irin ta Amurka ke fuskanta, na kutsa kai cikin dukkann fannonin masu alakar harkokin siyasa, da zamantakewar al’umma. Wadannan matsaloli sun tabbatar da cewa, dalilin da ya sa dimokuradiyya irin ta Amurka ba ta iya taka rawar gani kamar yadda ake fata shi ne, yanzu kasar ba ta samun kyawawan dabarun tafiyar da harkokin siyasa da ake bukata ba. (Amina Xu)