logo

HAUSA

Masu minshari ba sa barci yadda ya kamata

2023-03-20 08:31:28 CMG Hausa

 

Ranar 21 ga watan Maris a kowace shekara, rana ce ta yin barci ta duniya. Masana suna ganin cewa, yin minshari ba ya nufin yin barci mai zurfi, a’a kila akwai hadarin tsayawar numfashi a lokacin barci, tare da haifar da ciwon jijiyoyin zuciya da wasu cututtuka, har ma mutuwar ba zata. Don haka wadanda suke fama da mummunar mtsalar minshari, kamata ya yi su je ganin likitoci masu ilmin numfashi ko ilmin barci cikin lokaci.

Daya daga cikin masu minshari 5 ne na fama da matsalar tsayawar numfashi a lokacin barci sakamakon toshewar hanyoyin numfashi. Idan an yi ta tsayar da numfashi a lokacin barci, to, yawan iskar oxygen da ke jini zai ragu, lamarin da kila zai haddasa ciwon hawan jini, ciwon zuciya, shan inna, fid da jini daga kwakwalwa, ciwon sukari, ciwon bakin ciki, ciwon damuwa da dai sauransu, musamman ma mutuwar ba zata a lokacin sanyin safiya.

Ko da yake wajibi ne masu fama da mummunar matsalar tsayawar numfashi a lokacin barci su je ganin likita, hakika dai kalilan daga cikinsu ne sukan je ganin likita da kuma samun jinya. Yawancin mutane ba sa ayyana yin minshari a matsayin ciwo. Amma yin minshari ba ya nufin yin barci da kyau. Idan an yi minshari da babbar murya, a kan yi gumi da yawa sakamakon rashin yin numfashi, to, tilas ne a yi taka tsan-tsan kan yadda ake tsayar da numfashi a lokacin barci.

Likitoci sun shawarta cewa, zai fi kyau masu minshari su yi kwana a asibiti, a sa musu ido kan yadda suke barci a dare, don tattara bayanan barcin. Ban da haka kuma, a karkashin jagorancin likita, masu minshari su kan yi amfani da na’urorin zamani wajen sa ido kan yin minshari a lokacin barci a gida.

Masu karatu, idan ‘ya’yanku suna minshari, to, dole ne ku mai da hankali sosai. Saboda kananan yara masu koshin lafiya ba sa minshari. Yin minshari, wata alama ce ta gamuwa da matsalar lafiya. Kana kuma, yin minshari kan sauya fuskar kananan yara, wadanda suke girma a kowace rana.

Likitoci masu ilmin baka sun yi karin bayani da cewa, idan kananan yara suka dade suna numfashi, bakinsu a bude, ba sa shigar da iska daga hancinsu cikin dogon lokaci, to, hancinsu ba sa girma yadda ya kamata, baki dayan fuskokinsu za su sauya. Don haka ya zama tilas iyaye su mai da hankali kan ‘ya’yansu da suke minshari, su kai su asibiti don ba su jinya cikin lokaci. (Tasallah Yuan)