logo

HAUSA

Sojojin Nijeriya sun harbe dakarun kungiyar ISWAP 60

2023-03-20 14:05:09 CMG Hausa

Da sanyin safiyar jiya Lahadine wasu dakarun kungiyar ISWAP suka kai hari garin Mafa, na yankin karamar hukumar Mafa dake jihar Borno ta arewa maso gabashin Nijeriya, inda suka yi yunkurin kutsawa cikin cibiyar kidayar kuri’un zaben gwamnan jihar dake yankin, amma kafin su kai ga hakan sojoji sun bude musu wuta, inda nan take aka hallaka 60 daga cikin su.

Ban da wannan kuma, kakakin ‘yan sandan kasar Williams Ovye-Aya, ya bayyana cewa, a dai jiyan, ‘yan sanda suna kokarin ceto wasu mutane 6, wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su, yayin da suka kai hari kan ma’aikatan zabe a jihar Kogi dake arewa ta tsakiyar kasar.

Williams Ovye-Aya ya shaidawa wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, bayan gudanar da zaben majalisar dokokin jihar Kogi a ranar Lahadi, an kai hari kan ma’aikatan zaben, a kan hanyar su ta zuwa cibiyar kidaya kuri’un zaben dake Lokoja babban birnin jihar.

Ya ce ‘yan bindigar sun tare motar ma’aikatan a yankin Obajana, kuma sun yi awon-gaba da ma’aikata a kalla 6, kana sun raunata wasu mutanen yayin harin. (Zainab)