logo

HAUSA

Wace kasa ce za ta fuskanci asarar shekaru 20 da salon danniyar Amurka ke haifarwa?

2023-03-20 21:04:51 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Amurka ta yi amfani da karairayi wajen kaddamar da yaki kan Iraqi, matakin da ya haifar da mummunan bala’i ga Iraqi, da ma yankin gabas ta tsakiya. Kaza lika yakin ya gurgunta yanayin zaman lafiya da daidaito na duniya baki daya. Darasin dake tattare da hakan na da matukar jan hankali, ya kuma dace Amurka ta yi la’akari da shi, kuma duniya ta sanya lura kan hakan.

Wang Wenbin ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai da ya gudana a Litinin din nan, inda ya ce shekaru 20 da suka gabata, Amurka ta kaddamar da yaki kan Iraqi, bisa zargin kasar da mallakar makaman-kare-dangi, lamarin da ya haifar da kisan sama da fararen hular kasar 200,000, da raba sama da karin wasu miliyan 9 da muhallan su. Sai dai duk da haka, karin bayanan da suka fito fili sun nuna cewa, zargin gwamnatin Iraqi ta wancan lokacin da mallakar makaman-kare-dangi karya ce tsagwaron ta.   (Saminu Alhassan)