logo

HAUSA

Yaya kasar Sin ta sami babbar nasara yayin yaki da cutar COVID-19

2023-03-20 16:35:19 CMG Hausa

Shekaru 3 bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19 a duniya, kasar Sin tana mayar da jama’arta da rayukansu a gaban kome. Ta kuma kyautata matakan yaki da cutar bisa lokaci da yanayin da ake ciki. Tana kuma raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa da kuma dakile yaduwar cutar a lokaci guda, tare da kiyaye rayuka da lafiyar jama’arta yadda ya kamata.