logo

HAUSA

Dangantakar Sin da Rasha ta bayyana "hanyar da ta dace ta cudanya tsakanin kasa da kasa"

2023-03-20 21:55:11 CMG Hausa

Da yammacin ranar 20 ga watan Maris bisa agogon wurin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa birnin Moscow, don fara ziyarar aiki a kasar Rasha.

Wannan ita ce ziyara ta farko da Xi Jinping ya kai zuwa ketare, tun bayan da aka sake zabar sa a matsayin shugaban kasar Sin. Ana ganin cewa, hakan ya nuna irin muhimmancin da kasar Sin ke baiwa dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin ta da Rasha a sabon zamani. Dangantakar da ke tsakanin Sin da Rasha da ta fi girma, tana da amfani wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Sinawa kan ce, kamata ya yi a yi shiri, da tsare-tsare na dukkan shekara tun a farkon shekarar. An yi imanin cewa, ziyarar ta sada zumunci, da tabbatar da hadin gwiwa, da zaman lafiya da shugaba Xi Jinping ke yi a kasar Rasha za ta samu karin nasarori, kana kuma za ta sanya sabon kuzari ga ci gaban dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, da samar da karin moriya ga al'ummomin kasashen biyu, da kuma bada babbar gudummawa ga ci gaban duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)