Shugaban kasar Sin ya sauka a Moscow tare da gabatar da rubutaccen jawabi a filin jirgin sama
2023-03-20 20:34:06 CMG Hausa
Da yammacin Litinin din nan 20 ga wata ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya isa birnin Moscow, domin fara ziyarar aiki a kasar Rasha bisa gayyatar da aka yi masa.
Cikin rubutaccen jabawin da ya gabatar a filin jirgin sama, shugaba Xi ya ce, yau nake cika shekaru 10, bayan ziyarar aiki ta farko da na kawo Rasha a matsayin shugaban kasar Sin, inda tare da shugaba Putin na Rasha, muka bude sabon babin dangantakar kasashen biyu. Cikin shekaru sama da 10 da suka gabata, Sin da Rasha sun ci gaba da yaukakawa, da bunkasa alakar su bisa tushen rashin kulla kawance don mayar da wata kasa saniyar ware, da kaucewa fito na fito da kin far wa wani bangare na uku, sun kuma gina sabon salon alakar manyan kasashe bisa martaba juna, da zaman jituwa, da cimma moriyar hadin gwiwa. Ribar kyakkyawar dangantakar Sin da Rasha, ta haifar da moriya mai yawa ga al’ummun sashen biyu, tare da samar da gudummawa ga ci gaba, da bunkasar duniya baki daya.
Jawabin ya kuma fayyace cewa, Sin da Rasha dukkanin su manyan kasashen duniya ne, kuma mambobin dindindin a kwamitin tsaron MDD, wadanda ke taka muhimmiyar rawa a harkokin kasa da kasa. Yayin da ake fuskantar halin rashin tabbas da sauye sauye a duniya, Sin a shirye take ta ci gaba da aiki tare da Rasha, wajen kiyaye ka’idojin alakar kasa da kasa, da nacewa ci gaban dangantakar dukkanin sassa, da bunkasa akidar samar da ci gaba ta mahangar sassa daban daban, da gudanar da huldar kasa da kasa bisa dimokaradiyya, da yayata kyakkyawan jagorancin duniya bisa turbar adalci da dacewa.