logo

HAUSA

Firaministan kasar Djibouti ya mikawa tawagar jiyya ta kasar Sin lambar yabo

2023-03-20 15:10:55 CMG HAUSA

 

A madadin shugaban kasar Djibouti, firaministan kasar Abdoulkader Kamil Mohamed ya mikawa mambobi 12, na tawagar jiyya ta kasar Sin karo na 21, lambar yabo mai taken “Ranar samun ’yancin kan kasa, wato 27 ga watan Yuni”.

Yayin mika lambar yanon a jiya Lahadi, firaministan ya ce tawagar ta samu karbuwa daga masu samun jiyya, saboda da’ar ma’aikatan ta likitoci, da ingancin fasahohin su, da ruhinsu na bautawa jama’a. Ya ce gwamnatin kasar da jama’arta na matukar godiya game da hakan. Ya kara da cewa, yana mai fatan kasashen biyu za su kara hadin kai, don ingiza bunkasuwar kasashensu, a fannin ba da jiyya, ta yadda jama’a za su kara amfana. (Amina Xu)