logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sanadiyar mahaukaciyar guguwar Freddy da ta afkawa Malawi ya karu zuwa 477

2023-03-19 16:26:25 CMG Hausa

Sashen kula da bala'u na kasar Malawi ya bayyana cewa, adadin wadanda suka mutu sanadiyyar mahaukaciyar guguwar Freddy da ta afkawa yankin kudancin kasar, ya karu zuwa 477 ya zuwa karfe 7 na daren jiya Asabar agogon wurin, kana kimanin mutane 362,928 ne suka rasa matsugunansu. Yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 918, baya ga wasu 282 da suka bace. Ya zuwa yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyukan ceto. (Mai fassara: Bilkisu Xin)