logo

HAUSA

'Yan sandan Najeriya sun ceto jami'an zabe 17 da aka yi garkuwa da su

2023-03-19 16:38:50 CMG Hausa

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta bayyana cewa, ta yi nasarar ceto ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) guda 17, da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Imo da ke kudancin kasar a ranar Asabar din da ta gabata.

Mai magana da yawun hukumar zabe dake jihar Chinenye Chijioke-Osuji, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa, an yi nasarar ceto ma’aikatan ne, bayan kiran gaggawa da aka yi musu, da kuma muhimman bayanan da aka bayyanawa jami’an tsaro, inda nan  take suka bazama aikin ceto ma’aikatan da safiyar ranar Asabar.

Jami’an hukumar ta INEC dai, na kan hanyarsu ta zuwa rumfunan zabe 7 daban-daban dake jihar inda aka yi garkuwa da su. (Ibrahim)