Farfesa Yoro Diallo: Shawarar wayewar kai ta duniya tana da muhimmanci matuka
2023-03-19 14:46:37 CMG Hausa
A yayin babban taron tattaunawa tsakanin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyun siyasa na duniya da aka gudanar ta kafar internet a kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi jinping ya gabatar da shawarar wayewar kai ta duniya.
Dangane da shawarar da shugaba Xi ya gabatar, Yoro Diallo, shehun malami dan kasar Mali, kana darektan zartaswa na cibiyar nazarin harkokin kasashen Afirka masu amfani da harshen Faransanci, ta jami'ar koyon ilimin malanta ta lardin Zhejiang na kasar Sin, ya ce, wannan shawara tana da muhimmanci matuka, saboda ta nuna cewa duk wata kasar da tattalin arzikinta ke kan hanyar tasowa tana da cikakken ikon neman hanyar da ta dace da al'adunta da tarihinta, a kokarinta na zamanintar da kanta.
A cewar Farfesa Diallo, taron tattaunawar da aka gudanar tsakanin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da jam'iyyun siyasa na duniya, wani biki ne mai ma’ana sosai, ganin yadda dukkan jam'iyyun da suka halarci taron sun nuna buri na bai daya, wato kyautata zaman rayuwar jama’a. Ko da yake suna neman zamanintar da al’ummomimsu, amma maimakon a kwaikwayi baki dayan tsare-tsaren kasashen yamma, sun fi son kare al'adunsu masu daraja. Inda kasar Sin ta riga ta zama abin misali mai burgewa, wanda ya nuna cewa kowace kasa tana iya zamanintar da kanta, ta hanyar da ta zaba, wadda ta fi dacewa da yanayin da kasar ke ciki. (Bello Wang)