logo

HAUSA

Ofisoshin INEC na jihohi a tarayyar Najeriya sun fara karbar sakamakon zaben gwamna daga kananan hukumomi

2023-03-19 15:29:34 CMG Hausa

A ranar Asabar 18 ga wata, aka gudanar da zabukan gwamna da na ’yan majalissar dokoki a jihohi 28 daga cikin 36 dake fadin tarayyar Najeriya.

A halin yanzu an fara gabatar da sakamakon zaben gwamna ga ofisohin hukumar zabe na jihohin yayin da kuma sakamakon zaben ’yan majalissa ake sanar da shi a ofisoshin zaben kananan hukumomi kamar yadda dokar zabe ta tanadar.

Daga tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Miliyoyin ’yan Najeriya ne dai aka tantance yayin zaben na jiya Asabar domin kada kuri’arsu a cibiyoyin zabe 170,000.

Zaben na ranar Asabar an fara shi a kan lokaci sabanin wanda ya gabata na ranar 25 ga watan jiya, ko da yake dai fitowar mutane domin gudanar da zaben bai yi wani armashi a zo a gani ba a sassa daban daban kasar.

Wannan dai ba ya rasa nasaba da forofagandar tashe-tashen hankula da aka yi ta yadawa a shafukan sada zamunta gabannin zabe.

Da yawa dai sun fi shauki da farin cikin zabukan gwamnonin da na ’yan majalissun dokoki sabo da yanayin tasirinsu ga kyautatuwar rayuwar talaka.

Duk da dai hukumar zabe mai zaman kanta ta samu nasarar kaso 70 na zabukan da aka gudanar, amma dai akwai rahotanni dake nuna samun rigingimu nan da can a wasu runfunan zaben, yayin da kuma laifukan sayen kuri’u ya zama ruwan dare.

A dadin mutane 65 hukumar nan mai yaki da almundahnar kudade EFCC ta tabbatar da ta kama a lokacin da suke tsaka da sayen kuri’un jama’a.

Fargabar rashin tabbas na tsaro ya tilastawa hukumar zabe ta kasa dage gudanar da zabe a wasu cibiyoyi 10 dake Victorial Garden City a birnin Legos.

Alkaluman sakamakon zabukan sun fi karkata kan manya jam’iyyun 5 na kasar, wanda suka hadar da APC, da PDP, da Labour Party, da NNPP da kuma jam’iyyar APGA.

Zuwa dai yammacin ranar Lahadin nan hukumar zaben ta Najeriya za ta kammala fitar ta cikakken sakamakon zaben gwamnonin da ta gudanar wanda kuma za ta wallafa a shafinta na iREV, ya zuwa karfe 10 na daren jiya Asabar hukumar ta samu nasarar wallafa adadin sakamako 77,143. (Garba Abdullahi Bagwai)