Shugaba Buhari Na Tarayyar Najeriya Ya Sanya Hannu Kan Dokar Saukaka Harkokin Kasuwanci
2023-03-18 15:37:59 CRI
A ranar Alhamis 16 ga wata, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar da cewa babu tattalin arzikin da zai bunkasa ba tare da an bunkasa sha’anin samar da aikin yi da kuma kyautata bangaren kananan masana’antu ba.
Shugaban ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin ’yan majalissar gudanarwa na cibiyar kwararrun daraktoci ta kasa a fadarsa dake Abuja, inda ya ce, domin cimma wannan buri ne ma a kwanan nan ya rattaba hannu kan kudirin dokar saukaka harkokin kasuwanci.
Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.//////
Ita dai wannan cibiyar ta kunshi masana ne daban daban da suke kula da hukumomi da kamfanoni da suke bada gudummawa wajen ci gaban tattalin arzikin kasa, wadda kuma take karkashin jagorancin Dr. Mrs Ije Jidenma.
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa muddin ana bukatar habakar tattalin arzikin kasa cikin gaggawa lallai sai an sami tsayayyun kanana da matsakanta masana’antu a kasar.
Ya ce sabo da mahimmancin wadannan bangarori ne ya sanya duk da kalubalen da gwamnati ta yi ta fuskanta amma wannan bai hana ta yin namijin kokari ba domin tabbatar da bunkasuwar kanana da matsakantan masana’antun a Najeriya.
Shugaban kasar wanda ya bayyana wannan ziyara tasu da cewa ta zo a kan gaba domin a watan jiya ya sanya hannu kan kudirin dokar harkokin kasuwanci, dokar da za ta saukaka wa masu kananan sana’o’i da matsakanta wahalhalun da suke cin karo da su wajen gudanar da harkokinsu.
Ya ce yana da kyakkyawan fatan cewa wannan doka har ila yau za ta taimaka wajen inganta harkokin kasuwanci a kowane mataki.
Shugaba Muhammadu Buhari ya taya cibiyar murna cika shekaru 40 tana hidimar gina kasa tare da nuna dabi’u na gaskiya da adalci domin samar da kyakkyawan tsarin kasuwanci a kasa, inda ya bukaci masu ruwa da tsaki su yi kokarin cin gajiyar rawar da cibiyar za ta iya takawa wajen samar da ingantacciyar turbar bukasar tattalin arziki.
Shugaban kasar ya kara da cewa, “Yayin da tattalin arzikinmu da ma kamfanoni masu zaman kansu ke ci gaba da bunkasa, ya kamata masu ruwa da tsaki su gane cewa ba wai kawai ci gaba da wanzuwar wannan cibiya shi ne abin fata ba, lalle ne a ce tana da kayan aikin da suka kamata sannan kuma tana da karfin ba da tallafi domin ci gaban kasa.”
A nata jawabin, shugaban majalissar gudanarwar cibiyar Madam Ije Jidenma ta yaba ne bisa irin sauye-sauye daban daban da aka samu ta fuskar tattalin arziki a Najeriya cikin shekaru 8 da suka gabata, wanda wannan ya kara karfafa gwiwar ’yan kasuwa da shugabannin cibiyoyin kasuwanci mallakin gwamnati.
Mrs Ije ta kara jaddada kudirin cibiyar na bijiro da wasu matakai da za su kara kwarin gwiwa ga membobinta ta yadda za su kara sa kaimi a cikin ayyukansu. (Garba Abdullahi Bagwai)