logo

HAUSA

Demokiradiya Ba Kayan Ado Ba Ne

2023-03-18 16:44:17 CMG HAUSA

 

A wannan makon ne, aka kammala manyan taruka biyu na kasar wato, taron majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) da na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar (CPPCC), tarukan da suka kara fahimtar da kasashen duniya game da tsarin demokiradiyar kasar da yake damawa da daukacin al’ummar Sinawa.

Ta wannan cikakken tsarin ne, al’ummar kasar Sin da yawansu ya kai biliyan 1.4 ke bayyana ra’ayoyinsu, har su kai ga cimma matsaya da ma aiwatar da dukkan shawarwarin da aka cimma, inda daga karshe ke amfanar duniya baki.

Karkashin wannan tsarin ne, al’ummar Sinawa suka kudiri aniyar zamanantar da kasarsu, tare da samun ci gaba mai inganci.

Sanin kowa ne cewa, ci gaba mai inganci, tunani ne mai kyau, saboda ya hada ci gaba a fannonin kirkire-kirkiren fasahohi, da hakuri da bambancin ra’ayi, da kare muhalli, da kuma tabbatar da ci gaba mai dorewa. Kana, ci gaba mai inganci zai samar da muhallin rayuwa mai dorewa ga miliyoyin al’umma wanda, ba al’ummun Sinawa ne kadai za su ci gajiya daga ci gaba mai inganci na kasar ba, har ma da na duniya baki daya, domin zai ingiza bunkasuwar duk duniya ta hanyar gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, ciki har da kasashen Afirka.

 

Sabanin yadda wasu kasashen yamma ke daukar demokiradiya, masu fashin baki na cewa, demokiradiya ba kayan ado ba ne, kuma tsari ne na tilastawa wasu kasashe bin wani tsari ko tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe ba, amma tsari ne na warware matsalolin dake damun jama’a bisa yanayin da ya dace da yanayin kasashensu. Yadda al’ummar Sinawa suka nuna gamsuwa da gwamnatinsu, ya kara tabbatar da ingancin tsarin demokuradiyyar kasar, lamarin dake shaida cewa, demokuradiya irin na kasar Sin, na da kuzari, inganci matuka, kuma ya amsa sunansa. Domin bukatar kuku shi ne wanka. Kuma Sinawa sun gani a kasa. (Ibrahim Yaya)