logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sanadiyar mahaukaciyar guguwar Freddy da ta afkawa Malawi ya kai 438

2023-03-18 20:10:12 CMG Hausa

Sashen kula da bala'u ta kasar Malawi ya bayyana cewa, an yi nasarar gano karin gawarwaki a yankin kudancin kasar da guguwar Freddy ta afkawa, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu zuwa a kalla 438 ya zuwa karfe 9 na dare agogon wurin.

Kwamishinan kula da sashen Charles Kalemba ya bayyana cewa, kimanin mutane 345,183 ko kuma gidajen iyalai 79,602 ne suka rasa matsugunansu, kuma an kafa sansanonin 505 domin tsugunar da su. Yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 918, baya ga wasu 282 da suka bace. (Ibrahim)