logo

HAUSA

Yan jam’iyyun kasa da kasa sun yaba da jawabin Xi yayin taron tattaunawa

2023-03-18 15:54:06 CMG Hausa

Yan jam’iyyun kasashen duniya da dama sun bayyana cewa, jawabin da babban sakataren JKS Xi Jinping ya gabatar, yayin taron kolin tattaunawa tsakanin JKS da sauran jam’iyyun siyasa na kasa da kasa da aka kira ta kafar bidiyo, ya nuna ainihin burin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin na hada kai da jam’iyyu da kungiyoyjn siyasa na kasa da kasa, domin ingiza zamanantarwa da wadata da ci gaban duniya.

Babban sakataren jam’iyyar APC ta tarayyar Najeriya Iyiola Omisore yana mai cewa, babban sakatare Xi ya ambaci tunanin mayar da moriyar al’ummun kasa a gaban komai a cikin jawabinsa, tunanin da ya nuna cewa, JKS tana mai da hankali matuka kan moriyar al’ummun kasar a ko da yaushe.

Kana babban sakataren hadaddiyar jam’iyyar Islam ta kasar Iran Badam Zian ya bayyana cewa, kasar Sin tana kokari matuka wajen samar da rayuwa mai dadi ga al’ummar Sinawa, lamarin ba ma kawai ya amfanawa al’ummun kasar ta Sin ba, har ma zai amfanawa duniya baki daya. Kuma babban sakatare Xi Jinping ya gabatar da dabarun raya duniya, da shawarar tabbatar da tsaro a fadin duniya, da shawarar wayewar kai ta duniya, makasudin hakan shi ne gina wata duniya mai dadin zaman rayuwa da kwanciyar hankali, muna fatan za a cimma burin tabbatar da wadannan shawarwarin cikin nasara. (Jamila)