logo

HAUSA

Shugaban Pakistan: Tunanin gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya zai ciyar da zaman lafiyar bil Adama gaba

2023-03-18 15:12:43 CMG Hausa

A kwanakin baya ne, shugaban kasar Pakistan Arif Alvi ya zanta da wakiliyar CMG, inda ya bayyana cewa, tunanin gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, babbar gudummowa ce wajen shimfida zaman lafiya ga dukkan bil Adama a fadin duniya.

Shugaba Alvi ya yi tsokaci cewa, tunanin yana da ma’ana matuka ga daukacin al’ummomin kasashen duniya, saboda shugaba Xi ya gabatar da tunanin ne bisa tushen zaman lafiya, alal misali shawarar ziri daya da hanya daya, da shirin gina zirin tattalin arzikin dake tsakanin kasashen Sin da Pakistan, dukkansu suna bukatar kokarin da ake yi karkashin burin gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya.

Alvi ya kara da cewa, kasar Sin tana jagorancin ci gaban duniya bisa fitacciyar hanya, kuma kasar Sin ta nuna fifikonta wajen kawar da talauci, lamarin da ya zama abin koyi ga duk duniya, a don haka, ya dace a koyi darassin kasar Sin a wannan bangaren.

Ban da haka kasar Sin tana mai da hankali matuka kan aikin ba da ilmi da kiwon lafiya, kasar Pakistan ita ma tana yin kokari a bangarorin biyu kamar kasar Sin. (Jamila)