logo

HAUSA

Ana gudanar da zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a Najeriya

2023-03-18 20:04:00 CMG Hausa

A yau ne, Najeriya take gudanar da zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi. A wannan rana, jihohi 28 daga cikin 36 na kasar, za su zabi sabbin gwamnoni, yayin da sauran jihohi 8 kuma za su gudanar da zabe a lokuta daban-daban nan da shekaru 4 masu zuwa.  Za dai a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a dukkan jihohi 36 na kasar, jimillar ‘yan takara 10,231 suke neman kujeru 993 a majalisar dokokin jahohi 36 na kasar. (Ibrahim)