logo

HAUSA

Firaministan Sin ya bukaci a fara ayyukan da kafar dama

2023-03-18 16:33:32 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya bukaci da a yi kokarin aiwatar da shawarwari da tsare-tsaren kwamitin kolin JKS, da tabbatar da fara aiki mai kyau a wani sabon mafari.

Li ya bayyana hakan ne, yayin da yake jagorantar cikakken taron farko na sabon wa'adi na majalisar gudanarwar kasar Sin. Majalissar ta sanar da jadawalin ayyuka ga manyan jami’an majalisar kasa da kafa cibiyoyin majalisar kasa, tare da amincewa da sabbin ka’idojin aiki na majalisar da aka yi wa gyaran fuska, tare da shirya ayyukan gwamnati.

Li Qiang ya bayyana cewa, tsawon wa'adin shekaru 5 na wannan gwamnati, ya zo daidai da muhimmin lokaci na ganin an fara kokarin gina kasa mai ra'ayin gurguzu ta zamani daga dukkan fannoni. Yana mai cewa, manufar sabon wa'adin ita ce tabbatar da cewa, an aiwatar da shawarwari da tsare-tsare da kwamitin kolin JKS ya cimma bisa gaskiya da adalci

Bugu da kari, Li ya jaddada muhimmancin neman ci gaba mai inganci, a matsayin aiki na farko kuma mafi muhimmanci, inda ya bukaci da a yi kokarin ba da fifiko kan daidaiton tattalin arziki, da neman bunkasuwa cikin lumana, da aiwatar da manufofin da aka tsara bisa tsari da kuma niyya, da biyan bukatun cikin gida bisa ingantattun matakai, da ingiza bunkasuwar tattalin arziki baki daya. (Ibrahim)