Jaririn karkanda da jaririn jakin dawa suna yawo na yau da kullum
2023-03-17 09:39:06 CMG Hausa
A Mbombela na Afirka ta Kudu, jaririn karkanda mai suna Daisy da jaririn jakin dawa mai suna Modjadji suna yawo na yau da kullum. Dukkansu an ceto su ne suna jarirai marayu, daga wani wurin shakatawa na kasar a Afirka ta Kudu, kuma sun kulla abota ta kut da kut. (Bilkisu Xin)