logo

HAUSA

Sin ta gina rijiyar hakar mai da iskar gas mafi zurfi a nahiyar Asiya

2023-03-17 10:54:02 CMG Hausa

Assalamu alaikum, masu kallonmu. Kwanan nan, kasar Sin ta sake samun ci gaba kan shirin filayen hakar mai da iskar gas na Shunbei. Kamfani tace mai mafi girma na kasar Sin wato Sinopec ya sanar da cewa, zurfin rijiyar mai lamba 84 a sansanin Shunbei da ke doron kasa na Tarim a jihar Xinjiang ta kasar Sin ya zarce tsayin mita 8937.77, hakan ya sanya ta zama rijiyar mai mafi zurfi da aka hako a mike a doron kasa na nahiyar Asiya a halin yanzu.