logo

HAUSA

Ministan Harkokin Wajen Kasar Sin Da Takwaransa Na Ukraine Sun Yi Hira Ta Wayar Tarho

2023-03-17 13:45:26 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Qin Gang da takwaransa na kasar Ukraine Dmytro Kuleba sun zanta ta wayar tarho.

A yayin zantawar tasu jiya Alhamis Qin Gang ya ce, bayan da kasashen Sin da Ukraine suka kullar huldar diplomasiyya a tsakaninsu shekaru 31 da suka gabata, kasashen sun kiyaye ci gaban dangantakarsu. Kasar Sin na son hada kai da Ukraine wajen yin hangen nesa, da ci gaba da raya huldar da ke tsakaninsu ba tare da tangarda ba.

Kana Qin Gang ya yi karin haske kan matakai 4 da ya kamata a dauka wajen warware batun Ukraine, wadanda shugaba Xi Jinping ya gabatar, inda ya jaddada cewa, kasar Sin ba ta sauya matsayinta na nuna adalci da sanin ya kamata kan batun na Ukraine ba. Tana kuma himmantuwa wajen kara azama kan yin shawarwarin zaman lafiya, tare da yin kira ga kasashen duniya, da su samar da kyakkyawan sharadi na yin shawarwarin zaman lafiya a tsakanin bangarori masu ruwa da tsaki.

A nasa bangaren, Kuleba ya ce, kasar Sin, muhimmiyar abokiyar Ukraine ce ta fuskar yin hadin gwiwa, wadda ke taka muhimmiyar rawa a al’amuran kasa da kasa. Ya taya kasar Sin murnar sa kaimi kan samun sulhuntawa tsakanin kasashen Saudiyya da Iran a kwanan baya. Ya ce, Ukraine ta yi hangen nesa wajen daidaita huldar da ke tsakaninta da Sin, za kuma ta ci gaba da martaba manufar “kasar Sin daya tak a duniya”, da girmama cikakkun yankunan kasar, da inganta amincewar juna a tsakaninta da Sin da zurfafa hadin gwiwarsu a sassa daban daban.

Haka zalika, Kuleba ya yi karin bayani kan sabon yanayin rikicin Ukraine, da yiwuwar yin shawarwarin zaman lafiya. Ya kuma gode wa kasar Sin bisa yadda ta ba ta taimakon jin kai. Ya kuma yi bayani cewa, takardar matsayin Sin kan daidaita rikicin Ukraine a siyasance da ta gabatar, ta bayyana sahihancin sa kaimi kan tsagaita bude wuta da kawo karshen yaki. Don haka, ya yi fatan ci gaba da tuntubar kasar Sin. (Tasallah Yuan)