logo

HAUSA

Sana'ar tafiye-tafiye da yawon bulaguro tsakanin kasa da kasa ta kasar Sin tana kara samun farfadowa.

2023-03-17 11:37:45 CMG Hausa

Sakamakon barkewar annobar numfashi ta COVID-19, a farkon shekara ta 2020, an dakatar da shigowar masu yawon bude ido cikin kasar Sin daga kasashen waje, da fitar masu yawon bude ido daga kasar Sin zuwa kasashen ketare.  A watan Disambar shekarar da ta gabata, sakamakon kyautata matakan kandagarkin cutar da kasar Sin ta yi, musamman a fannin yawon bude ido, sana'ar tafiye-tafiye da yawon bulaguro  tsakanin kasa da kasa na kara samun farfadowa.