logo

HAUSA

Sin ta sanar da rage adadin kudin ajiya da ake bukata

2023-03-17 19:31:00 CMG Hausa

Babban bankin kasar Sin ya sanar a yau Jumma’a cewa, daga ranar 27 ga watan Maris, zai rage yawan adadin kudin ajiyar da ake bukata na cibiyoyin hada-hadar kudi da kashi 0.25, domin samar da isasshen kudi da kuma hidima ga sassan tattalin arzikin kasar.

Babban bankin ya ce, zai sanya manufofin hada-hadar kudi su dace kana masu tasiri, da yin amfani da manufofin hada-hadar kudi, da samar da isassun kudade, da tabbatar da kara samar da kudade ga jama’a, daidai da ci gaban tattalin arzikin. (Ibrahim)