logo

HAUSA

Dabarun Kasar Sin Kan Zamanantarwa

2023-03-17 13:29:02 CMG Hausa

Ranar 15 ga wata, a nan Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci babban taron tattaunawa tsakanin JKS da jam’iyyun siyasa na duniya a nan Beijing, tare da gabatar da jawabi, inda ya gabatar da dabarun kasar Sin na inganta zamanantar da duniya da kuma ci gaban wayewar kan daukacin bil-Adama.

Zamanantarwa, burikan kasa da kasa ne. Wane irin zamanantarwa muke bukata? Ta yaya za a samu zamanantarwa? Dangane da wadannan tambayoyi, shugaba Xi Jinping ya gabatar da ra’ayinsa a sassa biyar, kana ya yi nuni da cewa, ba tsirarrun kasashe ba ne suke da ’yancin samun damar zamanantar da kansu, kuma ba wata hanya daya kacal ba ce ta zamanantarwa. Toshe hanyar wasu, ba zai taimaka wajen samun ci gaba ba. Kamar yadda Xi ya fada, akwai wasu ka’idoji na zamanantarwa a duniya, amma wajibi ne wata kasa ta zamanantar da kanta bisa yanayin da take ciki, kuma bisa halin musamman irin nata. Dole ne ta tsaya tsayin daka kan samar da damarmaki da samun kyakkyawar makoma tare da sauran kasashe.

Yayin da ake zamanantarwa, wayewar kai irin daban daban na bil-Adama sun ba da muhimmiyar gudummawa. A yayin babban taron tattaunawar, karo na farko shugaba Xi Jinping ya gabatar da shawarar wayewar kai ta duniya, inda ya yi kira da a girmama kasancewar mabambantan wayewar kai a duniya, yayata akidun bai daya na ’yan Adam, sa muhimmanci kan gadon wayewar kai da yin kirkire-kirkire, da inganta mu’amala da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. Akasarin ra’ayoyin jama’ar kasa da kasa na ganin cewa, shawarar wayewar kan kasa da kasa, wani muhimmin tunani ne na daban da kasar Sin ta gabatar wa duniya, ban da tunanin raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam, shawarar raya duniya, da shawarar tsaron kasa da kasa.

Yayin da akwai tambayoyin da ake bukatar a ba da amsa dangane da zamanantarwa, wajibi ne jam’iyyu su ba da nasu amsa, a matsayin muhimmin ginshikan da ke jagoranta da kuma kaza azama kan aikin zamanantarwa. (Tasallah Yuan)