logo

HAUSA

Raya dangantaka tsakanin Sin da Rasha zai amfanawa duniya baki daya

2023-03-17 19:20:38 CMG Hausa

A yau ne, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya jagoranci taron namema labarai na yau kullum. Inda ya bayyana cewa, bunkasa dangantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, tsakanin kasashen Sin da Rasha ba wai kawai al’ummomin kasashen biyu za su amfana ba, har ma da duniya baki daya.

Ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai kasar Rasha, wata ziyara ce da za ta samar da zaman lafiya. Bangarorin biyu za su yi aiki da tsarin hadin gwiwa na gaskiya bisa ka’idojin rashin nuna son kai, da rashin takalar juna, da rashin hari ga bangarori na uku, da inganta alakar demokuradiyyar kasa da kasa, da ba da gudummawa don ci gaban duniya

Wang Wenbin ya bayyana cewa, game da batun Ukraine kuwa, kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan batun zaman lafiya, da tattaunawa, da daidaita tsari na tarihi. Takardar da aka fitar kwanan nan kan “Matsayin kasar Sin game da warware rikicin siyasar Ukraine” ta kunshi manufa da adalci na kasar Sin kan batun kasar Ukraine. Kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan wannan matsayi, za kuma ta taka rawar gani wajen inganta shawarwarin zaman lafiya.

Dangane da ziyarar da shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva zai kawo kasar Sin, Wang Wenbin ya ce, ya yi imanin cewa, wannan ziyara za ta sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin kasashen Sin da Brazil zuwa wani sabon matsayi, da bayar da sabbin gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da wadata a shiyyar da ma duniya baki daya. (Ibrahim)