logo

HAUSA

Mahaukaciyar guguwa ta halaka mutane 326 a kasar Malawi

2023-03-17 15:46:28 CMG Hausa

Ya zuwa jiya da dare, mutane 326 sun halaka, wasu 201 kuma suka bace kana 796 suka jikkata yayin da sama da dubu 180 suka rasa matsugunansu a kasar Malawi, sakamakon ambaliya da iska mai karfi da kuma zabtarewar kasa da mahaukaciyar guguwar Freddy ta haddasa.(Lubabatu)