logo

HAUSA

Sin ta samu jarin waje RMB Yuan biliyan 268.44 a watanni 2 na farkon bana

2023-03-17 19:40:25 CMG Hausa

Daga watan Janairu zuwa Fabrairu na wannan shekara, adadin jarin wajen da aka yi amfani da shi a fadin kasar, ya kai kudin Sin Yuan biliyan 268.44, karuwar kashi 6.1 cikin 100 kan na shekarar da ta gabata, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 39.71, wanda ya karu da kashi 1 cikin 100.

Dangane da sana’a, ainihin jarin wajen da aka yi amfani da shi a manyan masana’antu, ya karu da kashi 32 cikin 100, ciki har da kashi 68.9 cikin 100 da aka yi amfani da shi a masana’antun samar da kayayyaki da kuma kashi 23.3 cikin 100 a manyan masana’antun fasahar hidima. (Ibrahim)