logo

HAUSA

Xi ya ba da sabon tunani da shawarar wayewar kai ta duniya don inganta zamanantar da daukacin bil-Adama

2023-03-16 20:25:59 CMG Hausa

A yayin babban taron tattaunawa tsakanin JKS da jam’iyyun siyasa na duniya da aka gudanar, shugaban kasar Sin Xi jinping ya gabatar da sabon tunaninsa na inganta zamanantar da daukacin bil-Adama da kuma shawarar wayewar kai ta duniya.

A yayin wannan tattaunawar, shugaba Xi ya gabatar da shawarwari guda biyar, wadanda suka hada da yanayin zamanantarwa na jama’a, da bambancin hanyar da suka zaba, da ci gaba da tafiyar da tsarin, da daidaiton sakamakon da aka samu, da kuma tsayin daka na shugabanci.

Haka kuma, shugaba Xi ya gabatar da shawarar wayewar kai dake zama ta farko a duniya, wadda ta hada da: hadin gwiwa wajen ba da shawarar mutunta bambancin wayewar kai, da bayar da shawarar inganta dabi’un gama gari na dukkan bil-Adama, da ba da shawarar muhimmancin gadon wayewar kai, da kirkire-kirkiren wayewar kai, da hada kai don karfafa gwiwar kasa da kasa kan musaya da mu’amalar al’adu. (Ibrahim)