logo

HAUSA

Wakilin Sin na musamman ya karyata zargin dake cewa wai kasarsa na saka wa Afirka “tarkon bashi”

2023-03-16 13:25:39 CMG Hausa

Wakilin musamman a ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin mai kula da yankin kahon Afirka, Xue Bing, ya karyata kalamai marasa tushe dake cewa, wai kasar Sin tana saka wa Afirka “tarkon bashi”.

Xue, ya bayyana a shekaran jiya Talata a Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, cewa bai dace a dora wa kasar Sin laifin sanya wa Afirka bashi ba.

Alkaluman da bankin duniya ya fitar a bara sun nuna cewa, daga cikin bashin dala biliyan 696 da ake bin kasashen Afirka 49, kaso 75 bisa dari bashi ne na cibiyoyin hada-hadar kudi na bangarori daban-daban da ’yan kasuwan dake samar da bashi, abun da ya dauki akasarin bashin da ake bin kasashen Afirka. Kana akwai kaso 35 bisa dari na bashin da cibiyoyin samar da bashi masu zaman kansu na kasashen yammacin duniya ke bin kasashen Afirka, adadin da ya ninka kusan sau uku idan aka kwatanta da bashin da kasashen Afirka suka karba daga kasar Sin.

Domin taimakawa kasashen Afirka rage matsin lambar da suke fuskanta a fannin biyan bashi, kasar Sin ta shiga cikin “shawarar dakatar da biyan bashi” da kasashen G20 suka fitar, da rattaba hannu tare da kasashen Afirka 19 kan yarjejeniyar dakatar da biyan bashi, ko kuma cimma matsaya daya kan ragewa ko soke bashi baki daya. Amma akasin haka, wadanda suka fi sauran bangarori bayar da bashi ga kasashen Afirka, ciki har da masu samar da bashi masu zaman kansu na kasa da kasa, da cibiyoyin hada-hadar kudi na bangarori daban-daban, har yanzu ba su dauki matakan ragewa ko kuma soke bashin da suke bin kasashen Afirka ba.

A dayan bangaren kuma, Xue Bing ya ce, kasar Sin na goyon-bayan kasashen yankin kahon Afirka don su warware bambance-bambancen dake tsakaninsu ta hanyar yin shawarwari, da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a wannan yanki. (Murtala Zhang)