logo

HAUSA

Shirin wayewar kai na duniya wani muhimmin samfuri na jama’a ne da Sin ke samarwa ga al'ummomin duniya a sabon zamani

2023-03-16 21:25:08 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana Alhamis din nan cewa, shirin raya wayewar kai na duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar wani muhimmin samfurin jama’a ne da kasar Sin ta samar wa kasashen duniya a sabon zamani, bayan shirin raya kasa da kasa da shirin tsaro na duniya, wanda ya sa kaimi ga tsarin zamanantar da daukacin bil-Adama da gina al’umma mai makoma ta bai daya ga daukacin bil-Adama. (Ibrahim)