logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Nijer ya gana da ministan tsaron Nijar

2023-03-16 14:10:49 CMG Hausa

Jakadan Sin dake Nijer Jiang Feng ya gana da ministan tsaron jamhuriyar Nijer Alkassoum Indattou a jiya Laraba, inda suka yi musayar ra’ayoyi game da karfafa dangantakar abokantakar hadin gwiwa da hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu da inganta hadin gwiwa a fannin aikin soja.

Jakada Jiang ya bayyana cewa, a shekarun nan, dangantaka tsakanin Sin da Nijer ta samu bunkasuwa yadda ya kamata, kana an samu sakamako mai kyau a hadin gwiwar a aikace a fannoni daban daban. Bangaren kasar Sin yana son hada kai tare da Nijar, domin ci gaba da karfafa mu'amala da hadin gwiwa a fannin soji a tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a sa kaimi ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da sojojin kasar zuwa wani sabon matsayi.

Minista Indattou ya bayyana irin zumuncin da ke tsakanin Nijar da Sin, ya kuma godewa kasar Sin bisa taimakon da ta dade tana ba Nijar wajen gina kasa da ci gabanta. Ana sa ran kasar Sin za ta kara karfafa mu'amala da hadin gwiwa tsakaninta da kasar Nijar a fannin aikin soji bayan barkewar COVID-19, da taimakawa sojojin kasar wajen inganta karfinsu, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaba a yankin baki daya. (Safiyah Ma)