logo

HAUSA

Ministocin tsaron kasar Rasha da Amurka sun tattauna hatsarin jiragen yakin Amurka da ya faru a tekun Bahar Asuwad

2023-03-16 14:11:44 CMG Hausa

Shafin yanar gizo na ma'aikatar tsaron kasar Rasha ya fitar da sanarwar cewa, bisa bukatar Amurka, ministan tsaron kasar Rasha Shoigu ya tattauna ta wayar tarho da sakataren tsaron Amurka Austin a ranar 14 ga wata, inda bangaorin biyu suka yi musayar ra’ayoyi kan musabbabi da sakamakon hadarin.

Rahoton ya ce, Shoigu ya bayyana yayin tattaunawar cewa, dalilin faruwar lamarin shi ne, Amurka ba ta bi ka'idojin da suka dace na sanarwar da Rasha ta bayar na shata wuraren da aka kayyade jiragen sama a yayin gudanar da ayyukan soji na musamman, da kuma kara ayyukan leken asiri a kan muradun Rasha. 

Shawagin da jiragen yakin Amurka maras matuki suka yi a gabar tekun Crimea na da tada hankali, kuma zai iya dagula al'amura a yankin tekun Bahar Asuwad

Rahoton ya bayyana cewa, bangaren Rasha ba shi da sha'awar ci gaban lamarin, amma za ta ci gaba da mayar da martani ga duk wani mataki na yin tsokana. (Safiyah Ma)