Sin: Taimakawa yankin kahon Afirka ya kasance ginshikin zaman lafiya da hadin gwiwa da bunkasuwa tare
2023-03-16 19:43:00 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya jagoranci taron manema labarai na yau da kullum. Wani dan jarida ya yi masa tambayar cewa: Mene ne ra'ayin kasar Sin game da hadin gwiwa tsakanin kasashe da yankin kahon Afirka?
Wang Wenbin ya bayyana cewa, a halin yanzu, Habasha na kan wani muhimmin mataki na dawo da zaman lafiya, da mayar da hankali kan bunkasuwa. Mun yi imanin cewa, ya kamata dukkan kasashe su kara yin ayyukan da za su taimaka wajen ci gaban Habasha da samar da zaman lafiya a yankin baki daya, maimakon kakaba takunkumi don tilastawa ko tsoma baki a harkokin cikin gidan wasu kasashe kan wasu batutuwa masu sarkakiya. Kasar Sin tana son yin aiki tare da ragowar kasashen duniya, don taimakawa yankin na Afirka ya zama ginshikin zaman lafiya da hadin gwiwa da samun bunkasuwa cikin hadin gwiwa.
A dangane da batun kare hakkin bil Adama a kasar Amurka kuwa, Wang Wenbin ya ce, abin da ya dace gwamnatin Amurka ta yi shi ne, ta hanzarta magance matsalolin kare hakkin dan-Adam da ke kara ta’azzara a kasarta, kamar nuna wariyar launin fata, laifuffukan kyama, da matsalar harbin bindiga, da laifukan muggan kwayoyi da dai sauransu. (Ibrahim)