logo

HAUSA

Ziyarar shugaban gwamnatin Libiya Abdel Hamid Aldabaiba a Nijar

2023-03-16 13:54:23 CMG Hausa

A yanzu haka, kasashen Nijar da Libiya na cigaba da ingiza da ciyar da dangantakar kasashen biyu gaba, idan a ranar jiya Laraba, shugaban gwamnatin kasar Libiya, mista Abdel Hamid Aldabaiba ya sauka babban birnin kasar Nijar, tare da rakiyar mambobin gwamnatinsa da kuma manyan ’yan kasuwa kasarsa. Kasashen biyu, tun bayan mutuwar shugaba Mouammar Khaddafi suke kokarin farfado da huldarsu da daukar wata sabuwar alkibla.

Daga birnin Yamai, wakilinmu Maman Ada, ya aiko mana da wannan rahoto. 

Shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya gana a ranar jiya Laraba 15 ga watan Maris din shekarar 2023 tare da shugaban gwamnatin kasar Libiya, cewar da faraminista Abdel Aldabaiba a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai. Shugaba Bazoum ya tattauna tare da babban bako nasa kan halin dangantakar kasashen biyu, da kuma hanyar da kasashen biyu za su dauka domin ciyar da dangantaka tasu gaba, da kyautata zaman jituwa tsakanin al’umomin kasashen biyu da ke raba iyaka guda. Haka kuma kasar Nijar dai na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen ganin kasar Libiya ta koma bisa turbar tsarin mulkin demokaradiyya, da kuma ganin bangarori daban daban masu gaba da juna a kasar ta Libiya sun ajiye makamai domin gina kasarsu tare cikin zaman jituwa. Haka zalika, wannan ziyara ta faraministan kasar Libiya a babban birnin kasar Nijar na cikin tsarin shirye-shiryen bude bikin wani dandalin tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Nijar da Libiya, inda kamfanoni daban daban da masana’antu na kasashen biyu, da ma ’yan kasuwa na kasashen biyu za su nune-nunen kayayyaki iri daban daban kirar kasar Libiya da kasar Nijar domin ci gaban tattalin arziki da na kasuwanci na nahiyar Afrika musammun ma na kasashen biyu.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.