logo

HAUSA

Ziyarar gani da ido a lardin Zhejiang na kasar Sin

2023-03-15 09:58:22 CMG Hausa

A watan Faburairun bana, wakiliyarmu Faeza Mustapha ta kai ziyarci  wasu sanannun wurare 3, a garuruwa 3 dake lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin. Wadannan wurare uku su ne, tashar ruwa ta Ningbo-Zhoushan dake zaman irinta mafi girma a duniya, inda ta gani da idonta kan yadda ma’aikatan tashar ruwan suke amfani da fasahohin zamani, kamar fasahar 5G da tsarin ba da taswira na BeiDou, wajen sarrafa injuna daga nesa, suke jigilar kayayyaki sama da ton biliyan 1 a kowacce shekara, da jami'ar horas da malamai ta Zhejiang, da kuma cibiyar cinikayya ta duniya ta Yiwu. 

Sannan Faeza ta kai ziyara wata jami’ar da ta fi kowacce yawan dalibai ’yan Afrika a kasar Sin. Wannan jami’a ita ce jami’ar horar da malamai ta Zhejiang Normal University dake birnin Jinhua na lardin Zhejiang. Faeza ta ce, idan ake tafiya a titin birnin Jinhua, za a yi ta haduwa da ’yan Afrika da dama saboda wannan jami’a ta zama wani wurin dake matukar jan hanakalin ’yan Afrika. An ce wannan jami’a ce da ta horar da dalibai ’yan Afrika sama da 8000, ciki har da ’yan Nijeriya da dama.  

Baya ga haka, wata daliba Esther daga Najeriya ta jagoranci Faeza zuwa wani wuri mafi ban sha’awa, wato dakin adana kayayyakin tarihi dake cikin cibiyar nazarin harkokin nahiyar Afrika ta jami’ar, inda aka adana kayayyakin kasashen Afrika daban-daban sama da 1000, wadanda suka hada da zane-zane da kayayyakin waka da na addini da makamai da kayayyakin gona da sassaken katako da na dutse da tufafi da sauransu. Kuma ta samu damar haduwa da wanda ya assasa wannan daki wato daraktan cibiyar mai suna Farfesa Liu Hongwu. Farfesa Liu ya zagaya da ita wannan daki, har ya nuna mata wasu kayayyaki da shi da kansa ya dauko daga Nijeriya a lokacin da ya ziyarci kasar, har ma ya halarci bikin kamun kifi na Argungu Fishing Festival a jihar Kebbi. Farfesa Liu sannane ne kan harkokin Afrika a kasar Sin, wanda ya shafe kusan shekaru 30 yana nazarin Afrika, kana ya ziyarci kasashen Afrika sama da 20. 

Daga karshe dai, madam Faeza Mustapha ta kai ziyara cibiyar cinikayya ta duniya ta Yiwu dake garin Yiwu wanda ya yi fice wajen samar da kananan kayayyaki, kuma ya yi shahara a tsakanin ’yan kasuwar kasa da kasa, ciki har da na Nijeriya.

An ce wannan kasuwa na da girman muraba’in mita miliyan 6.4, kana akwai harkokin kasuwanci 7500, da kuma nau’ikan kayayyaki sama da miliyan 2.1, kama daga tufafi da kayayyakin gida da kitchen, zuwa kayayyakin wasa da na ado, da dai dukkan abubuwan da ake amfani da su na rayuwar yau da kullum. An yi kiyasin cewa, idan mutun zai yi yawo a kasuwar na tsawon sa’o’i 8 a kowacce rana, sannan ya kashe minti 3 a kowanne kanti, to zai dauki kimanin shekara daya da watanni 5 kafin ya kammala zagaye dukkan kantunan dake kasuwar.

Yiwu na da kyakkyawar alaka da kasashe da yankuna sama da 230 dake fadin duniya. Kuma nahiyar Afrika ta kasance kan gaba cikin jerin wuraren da suka fi karbar kayayyakin da aka fitar daga garin Yiwu. Bisa kiddidigar da hukumar kwastam ta garin ta fitar a shekarar 2022, darajar kayayyakin da aka yi shige da ficensu tsakanin Yiwu da nahiyar Afrika, ya kai kudin Sin yuan biliyan 84.02. 

Hakika gani ya kori ji, yadda Faeza ta ga tashar ruwa ta Ningbo-Zhoushan, da jami’ar horas da malamai ta Zhejiang, da cibiyar cinikayya ta duniya ta Yiwu, sun zarce abun da ta yi tunani da ma labaran da ta ji daga ’yan kasuwanmu na gida Nijeriya. A lardin Zhejiang, Faeza ta kuma gane mene ne “al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama” da shawarar “ziri daya da hanyar daya” suke nufi. (Faeza Mustapha, Ibrahim Yaya, Sanusi Chen)