logo

HAUSA

Amurka Da Birtaniya Da Australiya Sun Ci Gaba Da Shirinsu Kan Jirgin Karkashin Ruwa Mai Amfani Da Makamashin Nukiliya

2023-03-15 14:12:07 CMG Hausa

Ranar 13 ga wata, shugabannin kasashen Amurka, Birtaniya da Australiya sun gana tare da sanar da shirinsu na samar wa Australiya jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya.

Sanarwar hadin gwiwar da kasashen 3 suka bayar ta ce, Amurka za ta sayar wa Australiya jiragen karkashin ruwa masu amfani da makamashin nukiliya samfurin Virginia guda 3 a farkon shekaru 2030, daga baya kuma ta kara sayar mata jirage 2 na daban. Haka kuma kasashen 3 sun shirya nazarin wani sabon nau’in jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, bisa tushen fasahohin Amurka da Birtaniya. A cewar wani jami’in Australiya, za a kammala shirin baki daya a shekarar 2055, wanda za a kashe dalar Amurka biliyan 245 wajen aiwatarwa.

Kwanaki da dama kafin kasashen 3 su sanar da shirinsu, an gudanar da taron hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta IAEA na watan Maris a birnin Vienna, inda sakamakon kokarin da kasar Sin ta yi, an tattauna tare da nazarin batun hadin gwiwar da ke tsakanin Amurka da Birtaniya da Australiya kan jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, tsakanin mambobin hukumar karo na 7 a jere. Wasu kasashe sun nuna adawa kan hadin gwiwar kasashen 3. Amma kasashen 3 sun kau da kai daga damuwar kasa da kasa, sun ci gaba da sanar da shirin nasu, a yunkurin daukar matakin kashin kai, a maimakon cimma daidaito tsakanin bangarori daban daban, sun kara fadawa hanya mai hadari wadda kuma ba ta dace ba. Muddin aka aiwatar da shirinsu a zahiri, to, tabbas za a illata zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Asiya da tekun Fasifik, da yi wa tsarin hana yaduwar nukiliya na kasa da kasa barna, da sa kaimi kan yin takarar makamai, matakin da zai haifar da illoli masu dimbin yawa a nan gaba.

Hakika hadin gwiwar da ke tsakanin Amurka, Birtaniya da Australiya kan jirgin karkashin ruwa mai amfani da makamashin nukiliya, ba su ukun kadai ta shafa ba, tana da nasaba da muradun dukkan kasashe mambobin IAEA. Don haka, kamata ya yi mambobin IAEA su tattauna su kuma tsai da kuduri tare. Kafin a cimma daidaito kan wannan batu, bai kamata ba kasashen 3 su kaddamar da shirinsu. (Tasallah Yuan)