logo

HAUSA

Mujallar "Qiu Shi" za ta wallafa muhimmin sharhi da Xi ya rubuta kan ci gaban aikin gona

2023-03-15 19:15:29 CMG Hausa

Mujallar "Qiu Shi" da za a buga gobe Alhamis 16 ga watan Maris, za ta wallafa muhimmin sharhi da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta mai taken "Hanzarta aikin gona da inganta zamanantar da aikin gona da yankunan karkara".

Kasidar ta yi nuni da cewa, wajibi ne mu dora manufar gina kasa mai karfi a fannin noma tare da yin aiki mai kyau a aikin noma da yankunan karkara. Nan da shekarar 2035, za a kai ga nasarar zamanantar da aikin gona, kuma kasar Sin za ta zama wata kasa mai karfi a fannin aikin gona a tsakiyar wannan karni. Ya kamata mu tabbatar da samar da abinci cikin kwanciyar hankali da daidaito da muhimman kayayyakin amfanin gona, da inganta farfaɗo da kauyuka baki daya, da inganta zamanantar da kauyuka, da dogaro da kimiyya da fasaha da gyare-gyare don gaggauta gina kasar noma mai karfi.

Kasidar ta kuma yi nuni da cewa, ya kamata mu cimma manufar "Ainihin samun yanayin rayuwa na zamani a yankunan karkara", tsarawa da aiwatar da ayyukan gine-gine na karkara, da barin manoma su yi rayuwa ta zamani da wayewa nan take. Muddin ana son inganta zamanantar da yankunan karkara, ba kawai abin duniya ya kamata ya kasance mai wadata ba, ruhin rayuwa ma ya kamata ya zama mai wadata, da karfafa gina ruhin wayen kan yankunan karkara yadda ya kamata. (Ibrahim)