logo

HAUSA

Burtaniya ta yaba da zaben Najeriya duk da ’yan kura-kuran da aka samu

2023-03-15 10:51:02 CMG Hausa

Najeriya mai barin gado Catriona Laing ta bayyana zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan jiya a matsayin babbar shedar dake tabbatar da dauwamar mulkin demokradiyya a Najeriya.

Ta bayyana hakan ne lokacin da ta kai ziyarar ban kwana ga shugabannin majalissun dattawa da na wakilai na tarayyar Najeriya a birnin Abuja.

Daga Abuja a tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Madam Catriona Laing wadda ta jagoranci ofishin jakadancin kasar ta Burtaniya a Najeriya tun daga 2019 ta ce, babu shakka zaben ya burge matuka idan aka yi la’akari da na wasu kasashen dake nahiyar Afrika.

Madam Catriona ta kara da cewa zaben na ranar 25 ga watan jiya ya sake baiwa duniya tabbacin cewa tsarin shugabanci karkashin mulkin demokradiyya yana ci gaba da samun gindin zama a Najeriya.

Ta ce, duk da ’yan kura-kuran da aka yi ta cin karo da su a lokacin zaben , amma hakan bai hana samun nasarar da ake nema ba musamman ma wajen kare hakkin masu zaben tare da ragen matsalolin magudin zabe da rigingimun da ka iya tasowa bayan zabuka.

Jakadiyar kasar ta Burtaniya mai barin gado ta kara tabbatar da cewa zaben 2023 ya sha ban-ban da na 2019 ta fuskar inganci da tsari.

“Hakika Najeriya ta keto yanayi masu wahalar gaske kama daga annobar Covid-19 da matsalar tsaro da ya yi kamari a kusan kowane bangare na kasar, amma wannan bai kashe gwiwar ’yan kasar ba, wannan ni kaina ya kara tabbatar mun da kyakkyawar makomar da nake wa kasar fata.”

Ana sa jawabin shugaban Majalissar dattawan Najeriya Sanata Ahmad Lawan ya shaidawa jakadiyar Burtaniyar cewa duk nasarorin da Najeriya ke samu a fagen demokradiyya ya faru ne sakamakon irin gudumawar da ake samu daga Burtaniya kama daga bada horo da kuma bada shawarwari.

Da yake jawabi, a lokacin da ta ziyarce shi shugaban majalissar wakilai ta tarayyar Najeriya Mr Femi Bajabiamila cewa ya yi.

“Fatanmu a nan shi ne duk wanda zai kasance magajinki zai dora daga inda kika tsaya wajen kara gina kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Najeriya da Burtaniya, muna godiya matuka kuma za mu ci gaba da kewayarki.” (Garba Abdullahi Bagwai)