logo

HAUSA

Wakilan kamfanonin ketare 100 dake Sin sun halarci taron karawa juna sani game da ruhin tarukan biyu

2023-03-15 20:30:53 CMG Hausa

Kungiyar hulda da jama’a ta kasar Sin, da kungiyar kamfanonin kasar Sin masu jarin waje, sun gayyaci wakilan kamfanonin kasa da kasa fiye da 100 dake kasar Sin, domin gabatar da jawabi kan ruhin tarukan biyu da aka gudanar a nan birnin Beijing a ranar 15 ga wata, don taimakawa kamfanonin jarin kasashen waje, fahimtar yadda yanayin tattalin arzikin kasar Sin yake ciki, gami da manufofi da matakai daban-daban.

Mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sheng Qiuping ya bayyana cewa, duk da raguwar ci gaban tattalin arzikin duniya da aka samu a shekarar da ta gabata, yawan kudaden da kasar Sin ta samu daga kasashen ketare, ya karu. A shekarar 2022, ainihin jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi ya kai dalar Amurka biliyan 189.1, wanda ya karu da dalar Amurka biliyan 50, idan aka kwatanta da shekaru uku da suka gabata. Bayanai sun tabbatar da cewa, har yanzu kasar Sin ta kasance kasa mai karfin zuba jari a duniya.

Sheng Qiuping ya jaddada cewa, manufar kasar Sin ta yin amfani da jarin waje ba za ta sauya ba, kana kiyaye hakki da muradun kamfanoni masu jarin waje ba za su sauya ba, kana alkiblar samar da ingantacciyar hidima ga kamfanoni na dukkan kasashen duniya wajen zuba jari da fara kasuwanci a kasar Sin shi ma ba zai taba sauyawa ba. (Ibrahim)