logo

HAUSA

Tattaunawar Saudiyya da Iran da aka yi a Beijing nasara ce ta aiwatar da shawarar tabbatar da tsaro a duniya

2023-03-14 19:23:35 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce yadda kasa da kasa suka jinjinawa tattauanwar da aka yi tsakanin Saudiyya da Iran a birnin Beijing na Sin, ya nuna cewa samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa, buri ne na bai daya na kasashen yankin Gabas ta Tsakiya.

Wang Wenbin ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau, bayan an nemi jin ra’ayinsa game da yadda kasashe da dama na yankin Gabas ta Tsakiya suka yi maraba da tattaunawar da nasarorin da ta haifar.

Game da batutuwan da suka shafi tuntubar juna tsakanin Sin da Amurka kuwa, kakakin ya ce ya kamata Amurka ta nuna sahihanci ta kuma aiwatar da abubuwan da za su ingiza mayar da dangantakarta da Sin kan turbar da ta dace.

Wang Wenbin ya kara da bayyana matukar damuwa game da atisayen soja tsakanin Amurka da Korea ta Kudu. Ya ce yanayin da ake ciki a zirin Korea na sarkakiya. Ya ce ya kamata dukkan bangarori masu ruwa da tsaki su kai zuciya nesa tare da yin abubuwan da za su kai ga tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a zirin.

Ya kuma bayyana adawar kasar Sin kan kawancen Australia da Birtaniya da Amurka, na samar da sabbin jiragen ruwa masu amfani da makamashin nukiliya, yana cewa sun yi watsi da damuwar da kasa da kasa suka bayyana da barazanar yaduwar nukiliya da kawancen zai haifar. (Fa’iza Mustapha)