logo

HAUSA

Wasu shugabannin kasashe sun taya Xi Jinping murnar ci gaba da kasancewa shugaban kasar Sin

2023-03-14 11:03:50 CMG Hausa

 

Shugabannin kasashen duniya na ta mika sakwanni don taya Xi Jinping murnar ci gaba da zama shugaban kasar Sin.

A jiya ne shugaban kasar Zambia Hakainde Hichilema ya bayyana cewa, a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, kasar Sin tana ta taka muhimmiyar rawa wajen ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, yayin da take zama abun koyi ga sauran kasashe ta fuskar gyare-gyaren tsarin tattalin arziki. Ya ce yadda Xi ya ci gaba da zama shugaban kasar ya shaida cewa, al’ummar Sinawa na son ci gaba da bin hanyar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata da kuma bunkasuwa a karkashin jagorancinsa, yana mai cewa, bangaren Zambia na fatan kyautata huldar kud-da-kud a tsakaninsa da Sin.

A nasa bangaren kuma, Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya bayyana cewa, yadda aka zabi Xi a matsayin shugaban kasar Sin ya shaida imani da amincewa da al’ummar Sinawa ke nuna masa. Ya ce ana sa ran ganin kasar Sin ta kara samun manyan nasarori a karkashin jagorancinsa. Bugu da kari, shugaba Kagame ya ce ya na son hada kai da Shugaba Xi wajen ciyar da abotar dake tsakanin kasashen biyu zuwa gaba.

Bugu da kari, a cikin sakonsa, babban sakataren kungiyar kawancen kasashen Larabawa Ahmed Aboul Gheit ya ce, yadda Xi Jinping ya sake zama shugaban kasar Sin ya shaida yadda al’ummar Sinawa suka amince da shugabancinsa da kuma basirarsa ta tafiyar da harkokin kasa. Ya ce Kawancen kasashen Larabawa na son inganta dangantakar abota tsakanin bangarorin biyu bisa manyan tsare-tsare. (Kande Gao)