Kasar Sin za ta inganta zamanantar da cinikayyar hidimomi
2023-03-14 20:12:38 CMG Hausa
Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta ce za ta gaggauta aiwatar da sauye-sauye da daukaka dabaru da matakan bayar da hidima, da zamanatar da bangaren da bunkasa shi, da kara masa karfin takara da takwarorinsa na kasa da kasa.
Ma’aikatar ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai da aka yi yau, kan baje kolin cinikayyar hidimomi na kasa da kasa karo na 12 na kasar Sin.
A cewar ma’aikatar, za ta gaggauta aiwatar da gyare-gyare da inganta fasahohin bayar da hidima, ta yadda cinikayyar hidimomin za ta kara daraja da inganci da bunkasa ci gaban masana’antu masu ruwa da tsaki. (Fa’iza Mustapha)