logo

HAUSA

Ziyarar karfafa huldar dangantaka tsakanin kasashen Nijar da Benin

2023-03-14 09:56:47 CMG Hausa

A ranar jiya 13 ga watan Maris din shekarar 2023, shugaban jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya fara wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu a kasar Benin, tare da rakiyar ministoci da mambobin gwamanti bisa goron gayyatar shugaban kasar Benin Patrice Talon. Shugaba Bazoum da takwaransa na kasar Benin sun mai da hankali kan makomar huldar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Daga birnin Yamai, Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

A yayin wannan ziyara ta sa’o’i 48, shugaba Bazoum Mohamed ya yi ganawar kai tsaye a ranar jiya Litinin a fadar Marina dake birnin Cotonou tare da takwaransa na kasar Benin Patrice Talon, da kuma ganawar aiki tsakanin tawagogin kasashen biyu. Daga bisani taron manema labaru na hadin gwiwa ya gudana kan dukkan batutuwan da aka tattauna a yayin wannan ziyara.

Shugabannin biyu sun mai da hankali kan karfafa alakar hadin gwiwar tattalin arziki, da samar da ababen more rayuwa da kuma karfafa matakan tsaro ta dalilin kusancin yankunan biyu, ta yadda kasashen biyu za su hada karfi da karfe ganin yadda ita ma kasar Benin ta fara fuskantar karuwar hare-haren ta’addanci a kan iyakokinta daga arewa maso yammacin Burkina Faso. Matsalar da manyan jami’an biyu suka yi imanin kara karfafa dangantakar soja domin kawar da wannan annoba.

Daga karshe, shugaba Bazoum Mohamed da takwaransa Patrice Talon sun tabo batun tsarin aikin yarjejeniyar yankin Nijar da Benin, da irinsa ne na farko, da za a saka Sefa miliyan dubu 308, da kuma muhimmin batun tashar bututun  fitar da man fetur daga Nijar zuwa Benin, wanda shi ne mafi tsayi a Afirka. Wanda zai kwashi danyen mai na Nijar daga Agadem zuwa gabar ruwa ta Seme Krabe. Shugabannin biyu sun yi amani cewa wannan babban aiki zai ingiza tattalin arzikin kasashen biyu ta hanyar samar da dubban ayyukan yi a lokacin ayyukan da kuma bayansu.

Mamane Ada, sashen hausa na CRI daga Yamai a jamhuriyar Nijar.